Home Podcasts Dandalin Fasahar Fina-finai
Dandalin Fasahar Fina-finai

Dandalin Fasahar Fina-finai

RFI Hausa 24 Episodes Jun 20, 2026

Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya bai wa wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare da maimaici a ranar Lahadi da yamma.

Episodes

Tattaunawa ta musamman da mashiryin Fina-finai Abdul Amart Jun 20, 2026 00:20:00 A cikin shirin na wannan mako za ku ji mu ɗauke da tattaunawa ta musamman da mashiryin Fina-finai Abdul Amart.Muna tafe da batu kan fina-finan da aka fi tafka muhawara akan su cikin mako da muke bankwana da shi. Akwai mu da tattaunawa da Dauda Kahutu Rarara, wanda ya ballo sabuwar Dambarwa da mawaƙi Davido, da kuma yadda yake ganin wakokinsa na siyasa ka iya tasiri a zabe mai zuwa.
Karancin ingantaccen labarin fina-finai, lamarin da ke karya darajar su a Najeriya Nov 16, 2024 00:20:00 A cikin shirin na wannan mako a bangaren mu na Kannywood zamu duba yadda karancin ingantaccen labarin fina-finai, lamarin da ke karya darajar fina-finan. Za ku ji mu tafe da dambarwar da ta kunno kai tsakanin fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara, da hukumar tace fina-finai ta jijar Kano.
Korafe-korafen makallata fina-finan Hausa Jul 13, 2024 00:20:00 A cikin shirin na wannan mako, zamu sake yin waiwaye kan korafe-korafen makallata fina-finan Hausa, kan yadda mashirya fina-finai suka fi mayar da hankali kan soyayya, tare da fatali da sauran fannonin rayuwa.Za mu tsallaka Jamhuriyar Nijar, inda zamu duba yadda zamani yayi tafiyar ruwa da wake-waken ‘yan mata da ke tashe a baya.Muna tafe da tattaunawa da Hadiza Gire, guda daga cikin matan da suka
Ko ana 'kan ta waye' a masana'antar Kannywood? Feb 6, 2022 00:20:01 Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' ya yi nazari ne a kan al'amarin nan da ake kira 'kan-ta-waye'. Shirin ya yi  bayani a kan menene 'kan-ta-waye', sannan ya tattauna da baki, wadanda suka fadada bayanin don fahimtar mai sauraro.
Rayuwar mata masu shirya fina-finai a Nollywood a Najeriya Jan 30, 2022 00:20:00 A cikin wannan shirin na dandalin fasahar Fina-finai,Hawa Kabir ta samun tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Duniyar fina-finai dangane da makomar mata musaman a gidajen mazan su,ko wandada ke da niyar yin aure.
Halin da masana'antar Fim ta shiga a makon da ya kare Jan 9, 2022 00:20:00 Kamar yadda aka saba kowane mako shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai tare da Hauwa Kabeer ya tattauna akan wasu daga cikin muhimman al'amuran da ke wakana a masana'antar fina-fina da ke arewaci da kuma kudancin Najeriya.
Abinda ya wakana cikin kungiyar MOPAN a baya bayan nan Dec 19, 2021 00:20:00 Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon tare da Hauwa Kabeer, ya leka kungiyar MOPAN ne domin jin wainar da ake toyawa.
An kamala zaben wakilan kungiyar yan Fim a jihar Kaduna Dec 12, 2021 00:19:56 A cikin shirin duniyar fina-finai,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harakar fim yan lokuta bayan kamala zaben wakilan MOPAN a jihar Kaduna.Makomar duniyar Fim,hanyoyin kawo karshen baraka a wannan duniya na daga cikin manyan batutuwa da Hawa ta samu tattaunawa da bakin na ta.
Fitaccen makawaki ya sha alwashin daukar nauyin tallafawa mata da sana'o'i Dec 5, 2021 00:19:42 Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon tare da Hauwa Kabeer ya tattauna da wani fitaccen mawakin Hausa da ya sha alwashin daukar nauyin tallafawa mata da sana'o'i.
An fara daukar shirin 'Gidan Badamasi' zango na 4 Nov 21, 2021 00:20:00 Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai ya leka inda ake daukar shirin barkwancin nan mai dogon zango, wato 'Gidan Badamasi', inda ya gana da jarumai da masu ruwa da tsaki a shirin, cikin su har da babban daraktan shirin, Falalu Dorayi.
Rayuwar Alhaji Umaru Danjuma Katsina da aka fi sani da Kasagi Nov 7, 2021 00:20:00 Kasagi wanda ya rubuta fitaccen littafin da aka yi wa suna ‘Kulba na Barna’ ya rasu ne sakamakon gajeruwar rashin rashin lafiya.Danjuma Katsina na daya daga cikin fitattun masu wasan kwaikwayon da suka yi suna daga shekarar 1980 tare da wasu abokan aikin sa a lokacin irin su Kasimu Yero da Tumbuleke da Malam Mamman da karkuzu Na Bodara da kuma Samanja Mazan Fama. Hawa Kabir a cikin shirin dandalin
Masu ruwa da tsaki kan rubutun adabi da fina-finai na alhinin rasa Kasagi Oct 31, 2021 00:20:00 Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon tare da Hauwa Kabir ya tattauna na masu ruwa da tsaki kan rubutun adabin Hausa da kuma fina finai kan rasuwar marigayi Umaru Danjuma Katsina da aka fi sani da Kasagi.

Recommended