
Gaskiyar Magana
Gaskiyar Magana shiri ne na Hausa wanda ke tattauna harkokin siyasa, ra'ayin jama'a, da al'amuran al'umma. Jamilah Tangaza ce ke gabatar da shi, tana nazari da bayar da haske kan batutuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum. Shirin yana kawo tattaunawa kan siyasa da ra'ayin al'umma domin fahimtar abubuwan da ke faruwa a cikin al'umma. Ana sake duba ra'ayoyi da bayar da cikakken bayani kan al'amuran da suka shafi jama'a.
Episodes

Manyan Batutuwan Yakin Neman Zaben 2027
Menene manyan batutuwan da suka sha kan al’umma a lokacin Zaben 2027? Shirin yau, kashi na biyu ne na hira da Dr Aminu Isma’ila Sagagi, malami a Jami’ar Bayero dake Kano, kuma mai sharhi kan harkokin siyasar Najeriya.

Yaya Yakin Neman Zaben 2027 Ke Tafiya?
Tattaunawa da Dr. Aminu Ismail Sagagi, malami a Jami’ar Bayero da ke Kano kuma mai sharhi kan al’amuran rayuwa da siyasa, wanda ke bayyana damuwarsa kan salon yakin neman zaben 2027 da ake gani a Najeriya a yanzu.

Me Matasan 'Yan Siyasa Ke Cewa?
An jima ana cewa tsoffin hannu sun mamaye siyasar Najeriya. Amma yanzu matasan kasar sun yunkuro. Sai dai yaya manufofinsu su ka banbanta da wadanda suke kalubalanta? Ga hira da Hon. Bello Babajo, shugaban jam'iyyar APM na jihar Adamawa.

Hukuncin Kotun Koli Da Zaben Fidda Gwani
Wani hukuncin Kotun Koli na makon da ya gabata ya ja hankali. A shirin yau, mun tattauna da masanin shari’a a Najeriya Barrister Umar Isa Sulaiman dan jin takamaimai abin da wannan hukunci na Kotun Kolin ke nufi ga zaben 2027.

Me Matasan 'Yan Siyasa Ke Cewa?
A shirin yau mun tattauna da Hon. Bello Babajo, daya daga cikin matasan 'yan Najeriya da a yanzu haka ma shi ne shugaban jam'iyya a jiharsa. Ko yaya su ke kallon kamun ludayin magabatansu 'yan siyasa?

Yaya Jam'iyyu Su Ke Yakin Neman Zaben 2027?
A wannan shirin, Profesa Bello Bada, fitaccen masanin harkokin siyasa, kuma malami a jami’ar Usman Dan Fodio dake Sokoto, ya maida hankali kan dalilin da ya sa har yanzu ake batun kabila a zaben Najeriya.

INEC TA BUDE KOFAR YAKIN NEMAN ZABE
A yau, mun tattauna kan shirin jam’iyyun siyasar Najeria dangane da zaben 2027 da Profesa Bello Bada, fitaccen masanin harkokin siyasa, tarihi da al’adu, kuma malami a jami’ar Usman Dan Fodio dake Sokoto.

Me Ya Faru Bayan Fafutukar Kafa Dimokradiyya?
A wannan shirin mun tattauna da daya daga cikin wadanda suka yi fafutukar wanzar da dimokradiyya, Alhaji Abdulkarim Dayyabu, dan ji ko ya gamsu da yadda ake gudanar da tsarin dimokradiyya a Najeriya a yanzu?

Nasara Bayan Kalubale A Ilimi
A wannan kashi na hirata da Profesa Rahinatu, za mu ji yadda ta tunkari kalubale a matsayinta na mace, matashiya, bayan da ta yanke shawarar barin kasarta Najeriya dan neman ilimi.

Nasarar Ilimin Mata A Yau
A wannan shirin mun tattauna da Profesa Rahinatu Muazu, malama a Jamiar Kansas dake Amurka dan jin yadda tafiyarta ta kasance bayan an yi mata aure tana mai shekaru 15 a duniya.

MULKIN SOJE DA FAFUTUKAR WANZAR DA DIMOKRADIYYA A NAJERIYA
Tun daga mulkin turawan mulkin mallaka har zuwa mulkin soje. A shirin mu na yau mun tattaunawa da Alhaji Abdulkarin Dayyabu, shugabqn Kungiyar Rundunar Adalci, dan jin abin da ya sa suka dage dan ganin sun kori sojoji daga mulkin Najeriya.

HASARA: KAURAR KWARARRU DAGA NAJERIYA
Najeriya na tafka hasara inda kwararrunta ke ficewa daga kasar. A wannan shirin na Gaskiyar Magana, mun tattauna da Profesa Zubaida Farou-Ladan, malamar koyar da aikin likita a Jami’ar Bayero dake Kano, dan jin yadda su ke ji a game da guduwa daga Najeriya da likitocinsu ke yi zuwa kasashen waje.

ILIMIN MATA: NASARORI DA KALUBALE
A wannan shiri, mun duba sauyin da aka samu na bai wa ‘ya’ya mata karatu a kasar Hausa kamar Kano. Na tattauna da Profesa Zubaida Farouk Ladan, likitan yara, kuma malama a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dan jin yadda tafiyarta a ilimin boko, ta kasance.

FASAHAR SADARWA: SAUYE-SAUYE A AL'ADAR HAUSAWA
Shin Fasahar Sadarwa ta Zamani ta na tasirri kan a al'adun Hausawa a yau, ko kuwa dama wadannan halayyar mu ce? A wannan shirin mun tattauna da Profesa Maryam Mansur Yola, malama a fannin al'adu ta Jami'ar Bayero dake Kano.

Tarbiyya: Bangaren Addini Da Zamani
Shin akwai dangantaka tsanin addinin Musulunci da al’adun Hausawa? A yau na tattaunawa da Dr Usman Ahmad Mustapha, malamin Shari’ar Musulunci a Kwalejin Koyar da Shari’ar Musulunci da Ilimin Addini ta Kano.

Al'adun Hausa A Zamanin Yanzu
Ko kutsowar bakin al’adu na barazana ga al’adun Hausawa a wannan zamani da muke ciki? Yau na tattauna da Profesa Maryam Mansur Yola, kwararriya a fannin al’adu a Jami’ar Bayero dake Kano.

Tasirin Sauyin Yanayi Ga Samar Da Abinci
Ko me masana ke cewa a game da barazanar sauyin yanayi wajen samar da wadataccen abinci? A yau mun tattaunawa da Profesa Amina Mustapha ta fannin tsimi da tanadi na aikin goma na Jami’ar Bayero dake Kano.

Bangaren Shari'a Da Yancin Tsayawa da Kafafunsu
A yayinda ake shirin zaben 2027, babbar tambaya ita ce: Anya ‘yan bangaren shari’a zasu iya tsayawa da kafafunsu? Mun tattauna da fitaccen lauya a Kano Barista Umar Isa Suleiman.

Tarbiyya a Yau: Zamani Ko Damuwa?
Hira da Dr Aminu Ismai’il Sagagi, malami a jami’ar Bayero dak Kano kuma mai sharhi kan harkokin yau da kullum kan tarbarewar tarbiyya a yankin Arewa a yanzu.

Tiriliyan Nawa? Bashin Da Ke Kan Najeriya
Fitaccen masanin tattalin arziki, Dr. Abdussalam Kani, ya ce cin bashi ga Najeriya ba laifi ba ne. Amma akwai wata babbar damuwa ta daban. Shin mecece wannan matsalar?

Tarihin Noma A Arewa
Tattaunawa da Profesa Amina Mustapha, kwararriya a fannin tsimi da tanadi na aikin noma, dan jin tarihi da matsayin noma a Arewan Nigeria, inda mafi yawan al’ummunta manoma ne.

Tattalin Arzikin Najeriya A Yau
Dr Abdussalam Kani, fitaccen masanin tattalin arziki a kasar ya bayyana ainihin abubuwan da suka sa Najeriya ke fama da matsalolin tattalin arziki.

Matsayin Bangaren Shari'a A Dimokradiyya
A shirin mu na yau, Barista Umar Isa Suleiman fitaccen lawya a Najeriya, ya bayyana matsayin bangaren shari’a a tsarin dimokradiyyar Najeriya da irin kalubalen da ya ke fuskanta.

Hukumar Bogi: Gaskiya Ko Al'mara?
Hukumar bogi da ake zargin wani mutum mai suna Adeniyi Adeyemi ya kafa a Najeriya na ci gaba da janyo cece-kuce. A wannan shirin, mun tattauna da Dr. Aminu Isma'il Sagagi, malamin jami'a kuma fitaccen mai sharhi kan wannan batun.

Yanayin Noma Yanzu A Nigeria
A shirin yau na Gaskiyar Magana, Alhaji Hamisu Ahmed Uba, Sarkin Kasuwar abinci ta Dawanau dake Kano, ya ce har yanzu, akwai fata a harkar noma duk da matsalar rashin tsaro a wasu sassan Najeriya.

Sai An Ceto Kasuwancin Arewa
A wannan shirin, Alhaji Sa'idu Adhama ya bayyana cewa dole sai an tallafawa masana'antu a Arewa da Kano, muddin ana san bukasa tattalin arzikin yankin.











