Home Podcasts Lafiya Jari ce
Lafiya Jari ce

Lafiya Jari ce

RFI Hausa 24 Episodes Sep 7, 2026

Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama'a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.

Episodes

Illar da ke tattare da shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba
Illar da ke tattare da shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba Sep 7, 2026 00:10:14 Shirin lafiya jari ce a wannan karon ya mayar da hankali kan ɗabi'ar shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba, wanda a turance ake kira Self-medication da kuma illar hakan ga lafiyar jama’a. Wasu alƙaluma sun nuna cewa fiye da kashi 70 cikin ɗari na ƴan Najeriya ne yanzu haka sun bijirewa ziyartar asibitoci ta yadda suke shan magungunan tarin cutuka ba tare da umarnin ƙwararru ba, mus
Yadda cutar damuwa ke zama ruwan dare a tsakanin al'umma
Yadda cutar damuwa ke zama ruwan dare a tsakanin al'umma Aug 24, 2026 00:09:58 A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce zai yi duba ne kan lalurar Depression ko kuma damuwa mai tsanani a harshen hausa, cutar da ke ƙoƙarin zama ruwan dare tsakanin al’umma a baya-bayan nan, wataƙila ko saboda yanayi da matsin rayuwa. Ku danna almar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
Yadda wuraren saida magunguna ke samun karbuwa a jamhuriyar Nijar lokacin damuna
Yadda wuraren saida magunguna ke samun karbuwa a jamhuriyar Nijar lokacin damuna Aug 17, 2026 00:10:01 Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya leƙa jamhuriyyar Nijar inda ya yi dubi kan yadda ake samun kafuwar wuraren saida magunguna birjik musamman a lokaci irin na damuna, wato dai lokacin da ake ganin yawaitar cutuka irin zazzaɓin cizon sabro. Danna alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....
Yadda cutar kwalara ta jefa ɗumbin mutane cikin firgici a jihar Bornon Najeriya
Yadda cutar kwalara ta jefa ɗumbin mutane cikin firgici a jihar Bornon Najeriya Aug 10, 2026 00:09:56 A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan sake ɓarkewar cutar kwalara ko kuma amai da gudawa a jihar Borno, lamarin da ya jefa ɗimbin jama’a a yanayi na matuƙar damuwa damuwa musamman bayan da rahotanni ke cewa an samu yaɗuwar annobar cutar har a yankunan da ake ajje da ɗimbin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu.
Yadda cutar Bilharzia ko Tsagiya ke barazana ga rayuwar ɗimbin ƴan Afirka
Yadda cutar Bilharzia ko Tsagiya ke barazana ga rayuwar ɗimbin ƴan Afirka Aug 3, 2026 00:10:00 A wannan makon shirin na lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba duba kan cutar Schistosomiasis (shustosumayusus) ko Bilharzia koma Snail fever kamar yadda wasu ke kiranta, cutar nan dai da aka fi sani da tsagiya a hausance, cutar alƙaluma ke nuni da cewa kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da ita na a nahiyar Afrika. Shiga alamar sauti don sauraron karin bayani.......
Yadda farashin magunguna ke tashi a lokacin damuna da aka fi fama da cutuka
Yadda farashin magunguna ke tashi a lokacin damuna da aka fi fama da cutuka Jul 27, 2026 00:09:59 Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya yi dubi ne kan yawaitar cututtuka a irin wannan lokaci na damuna, daidai lokacin da bayanai ke nuni da cewa farashin magunguna ya yi tashin gauron zabbi. Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Azima Bashir Aminu...
Yadda gwamnatin Kano ta yi nasarar rage mace-macen mata a lokacin haihuwa
Yadda gwamnatin Kano ta yi nasarar rage mace-macen mata a lokacin haihuwa Jul 20, 2026 00:10:05 Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu  ya mayar da hankali kan nasarar da jihar Kano ke iƙirarin samu bayan fitar wani rahoto da ke cewa an samu raguwar mace-macen mata a lokacin haihuwa a sassan jihar wadda a baya ke sahun gaba wajen asarar rayukan ɗimbin mata a lokacin haihuwa ko goyon ciki Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin..........
Matsalar ƙarin mahaifa ko fibroids ga lafiyar mata
Matsalar ƙarin mahaifa ko fibroids ga lafiyar mata Jul 13, 2026 00:10:08 Shirin Lafiya Jari Ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar ƙaba ko ƙarin mahaifi ko kuma fibroids da ke addabar tarin mata ta yadda da dama ke rayuwa da shi ba tare da sani ba, yayinda wanzuwarsa a mahaifa kan haddasa matsala ga yanayin haihuwa ga matan. Galibi mata a tsakanin shekaru 35 zuwa 37 ne suka fi kamuwa da wannan lalura ta Fibroids, a wani yanayi da ƙidi
Yadda cutar Typhiod ke barazana ga rayuwar miliyoyin mutane a Afirka da Asiya
Yadda cutar Typhiod ke barazana ga rayuwar miliyoyin mutane a Afirka da Asiya Jul 6, 2026 00:10:10 Shirin na Lafiya Jari ce zai  a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan zazzaɓin Typhoid, cuta mai haɗari wadda ƙwayar cutar Salmonella Typhi ke haddasawa, inda ta kan yaɗu ta hanyar abinci ko ruwan da ya gurɓata. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
Ƙaruwar masu fama da cutar sikila a Jamhuriyar Kamaru
Ƙaruwar masu fama da cutar sikila a Jamhuriyar Kamaru Jun 29, 2026 00:10:08 A wannan makon shirin ya yi duba ne kan ƙaruwar masu fama da cutar sikila a jamhuriyyar Kamaru bayan fitar wani rahoto da ke cewa cikin shekara 1 kaɗai an tattara alƙaluman sabbin mutum dubu 6 da aka gano suna ɗauke da cutar. Wannan cuta mai alaƙa da nau’in jini, na daga cikin matakan yaƙi da ita shi ne tabbatar da gwaje-gwajen jini tun kafin aure don kaucewa haifar yara masu ɗauke da ita, ganin c
Illolin da ke tattare da sauya launin fata da wasu mata ke yi
Illolin da ke tattare da sauya launin fata da wasu mata ke yi Jun 8, 2026 00:10:11 Shirin lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda mata suka rungumi tsarin gyaran jiki ta fannoni daban-daban kama daga magungunan sha ko mayukan shafawa ko kuma salon amfani da na’ura da nufin ƙawata sura. Wasu daga cikin batutuwa mafi jan hankali a wannan babi na gyaran jiki shi ne tayar da komaɗar fata da sauran sassan jiki don killacewa ko kuma kange kai daga bayyanar tsufa, k
Illolin magungunan matsi ga lafiyar mata
Illolin magungunan matsi ga lafiyar mata Jun 1, 2026 00:10:06 Shirin a wannan mako zai ɗora ne akan wanda ya gabace shi a makon jiya, sai dai a wannan karon zamu karkata ga illolin da magungunan matsi ke haifarwa ga lafiyar mata, duk da ya ke matan kan yi don bajinta ko nuna isa a wajen mazajensu. Danna alamar sauti don sauraron karin bayani.....

Recommended