Home Podcasts ADPlusHausa | Podcast
ADPlusHausa | Podcast

ADPlusHausa | Podcast

ADPlusHausa | Podcast 78 Episodes Aug 23, 2026

Sashen podcast na Afrika. Fagen tattaunawa da batutuwa da suka shafi al'adu. Muna bawa mazauna Afrika masu magana da harshen Hausa muhimmanci a dukkan lamuran rayuwarsu. Shiri ne da ke karkashin kafafen sadarwa na Afrika.

Episodes

57 | SHIN AURE MAKABATAR SOYAYYA NE? | MAL. LAWAN ADAM GIGINYU
57 | SHIN AURE MAKABATAR SOYAYYA NE? | MAL. LAWAN ADAM GIGINYU Aug 23, 2026 03:40:53 IYALI SU NE GINSHIƘIN AL’UMMA; IDAN GIDA YA GYARU, AL’UMMA MA ZA TA SAMU GYARA. GINA IYALI NAGARI BA YA TSAYAWA GA SAMUN KUƊI KO ZAMA TARE KAWAI, A’A, YANA BUƘATAR SOYAYYA, FAHIMTAR JUNA, MUTUNTA JUNA, HAƘURI, AMANA DA KYAKKYAWAR TARBIYYA. A YAU ZA MU TATTAUNA MUHIMMAN RUKUNAN DA AKE BUƘATA WAJEN GINA IYALI NAGARI, DA KUMA WASU ƘALUBALEN DA KAN KAWO RASHIN JITUWA TSAKANIN MA’AURATA DA SAURAN ’YAN
56 | SHIN RASHIN TARBIYYA NE KE RUSHE SHUGABANCI A NAJERIYA DAMA AFRIKA? | PROF. USMAN BUGAJE
56 | SHIN RASHIN TARBIYYA NE KE RUSHE SHUGABANCI A NAJERIYA DAMA AFRIKA? | PROF. USMAN BUGAJE Aug 9, 2026 00:45:32 “Shugabanci na Gari a Tsarin Dimokuraɗiyya.” Shugabanci ba mulki kawai ba ne, illa amana ce, nauyi ne, da kuma hidima ga jama'a. A tsarin dimokuraɗiyya, ana bai wa 'yan ƙasa damar zaɓar shugabanninsu, amma tambayar ita ce: ta yaya za mu tabbatar da cewa wannan zaɓe yana haifar da shugabanci mai adalci, gaskiya, amana da bin doka? A yau za mu duba ginshiƙan shugabanci na gari, rawar shugaba
55 | ZUBA JARI A TSARIN MUSULUNCI DA ABIN DA YA KAMATA KA SANI | DR. NABIL BELLO SA'ID, MD KONOOZ
55 | ZUBA JARI A TSARIN MUSULUNCI DA ABIN DA YA KAMATA KA SANI | DR. NABIL BELLO SA'ID, MD KONOOZ Jul 26, 2026 03:43:42 A yau mutane da dama suna son su zuba jari domin su ƙara samun kuɗi, amma rashin ilimi yana sa wasu su yi asara ko kuma su faɗa cikin hanyoyin da ba su dace ba.A wannan shiri na Rumfar Africa Podcast Hausa, kashi na (55) za mu tattauna muhimman ƙa'idojin da ya kamata kowane mai son zuba jari ya sani, tare da ƙwararren masani a fannin tattalin arziki, zuba jari da Islamic Finance, Dr. Nabil Bel
54 | MATASA DA SON YIN KUƊI A GAGGAUCE: HANYAR ARZIKI KO TARKO? | PROF. MUNIR ABDULLAHI KAMBA
54 | MATASA DA SON YIN KUƊI A GAGGAUCE: HANYAR ARZIKI KO TARKO? | PROF. MUNIR ABDULLAHI KAMBA Jul 12, 2026 02:08:21 MATASA DA SON YIN KUƊI A GAGGAUCE: HANYAR ARZIKI KO TARKO?Domin yin nazari a kan wannan batu, muna tare da babban baƙonmu, Farfesa Munir Abdullahi Kamba, wanda zai yi mana bayani kan tushen wannan matsala, illolinta, da kuma hanyoyin da matasa za su bi wajen gina arziki cikin hikima da dorewa.
53 | YAƘI KO SULHU? MAKOMAR RIKICIN IRAN, AMURKA DA ISRA'ILA | DR. RAYA'UDDEEN ZUBAIR MAITAMA
53 | YAƘI KO SULHU? MAKOMAR RIKICIN IRAN, AMURKA DA ISRA'ILA | DR. RAYA'UDDEEN ZUBAIR MAITAMA Jul 5, 2026 03:45:56 Shin ana iya warware wannan rikici ta hanyar yaƙi, ko kuwa mafita tana cikin tattaunawa da diflomasiyya?-------------------------------------A yau duniya na ci gaba da sa ido kan rikicin da ke tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila. Tashin hankali na ƙaruwa, hare-hare na ci gaba, yayin da duniya ke tambayar kanta: Shin wannan rikici zai tsaya a nan, ko kuwa zai rikide zuwa babban yaƙin yanki? Mene
ME KE FARUWA A KASASHEN SAHEL (NIGER, MALI DA BIRKINA FASO) | DR. RIYA'UDDEN ZUBAIR MAITAMA
ME KE FARUWA A KASASHEN SAHEL (NIGER, MALI DA BIRKINA FASO) | DR. RIYA'UDDEN ZUBAIR MAITAMA Jun 28, 2026 00:16:36 TAKAITACCEN SHARHI A KAN ABINDA KE WAKANA A KASHEN SAHEL, TARE DA MASANIN KIMIYYAR SIYASA DA SHA'ANIN MULKI
52 | DA’AWAR MUSULUNCI DA BIBLE | SH. ALIYU MUHAMMAD RABI'U (ALI DEEDAT) | RUMAFAR AFRICA PODCAST
52 | DA’AWAR MUSULUNCI DA BIBLE | SH. ALIYU MUHAMMAD RABI'U (ALI DEEDAT) | RUMAFAR AFRICA PODCAST Jun 14, 2026 03:41:31 Da’awar Musulunci da Bible: Hanyoyin Isar da Saƙon Musulunci ga Mabiyan Kiristanci.Ta yaya Musulmai za su yi da’awa cikin hikima da fahimtar addinin Kirista? Wane matsayi Bible take da shi a tattaunawar addinai? Kasance tare da mu domin jin tattaunawa mai zurfi kan hanyoyin gina fahimta, mutunta juna da kuma isar da saƙon Musulunci cikin basira da hikima.
51 | HAJJI MAKARANTAR SHUGABANCI | IMAM, DR. MUHAMMAD SULAIMAN ADAM
51 | HAJJI MAKARANTAR SHUGABANCI | IMAM, DR. MUHAMMAD SULAIMAN ADAM Jun 8, 2026 03:50:12 “HAJJI: MAKARANTAR SHUGABANCI”Shin wane darasi shugabanni da al’umma za su koya daga hajji? Ta yaya hajji ke koyar da tsari, adalci, tawali’u da haɗin kai?Domin tattauna wannan batu, muna tare da babban bako:IMAM, DR. MUHAMMAD SULAIMAN ADAM.
50 | SANA'AR JARI BOLA A DUNIYA | ENGR. ALIYU SABO YA KASAI | BABBAN MAI SANA'AR JARI BOLA
50 | SANA'AR JARI BOLA A DUNIYA | ENGR. ALIYU SABO YA KASAI | BABBAN MAI SANA'AR JARI BOLA May 17, 2026 04:21:12 Sana’ar Jari Bola ta zama ɗaya daga cikin sana’o’in zamani da suka mamaye duniya, tana jan hankalin miliyoyin mutane saboda damar samun riba cikin gajeren lokaci. Amma a bayan nasara akwai ƙalubale, haɗari da dabarun da ke buƙatar ilimi da ƙwarewa. A wannan shiri na musamman, za mu tattauna kan nasarorin sana’ar, ƙalubalen da masu ita ke fuskanta, hanyoyin inganta ta a wannan zamani, da kuma yadda
49 | YAƘIN ISRA'ILA DA IRAN DA KUMA NAHIYAR AFRICA | DR. RIYA'UDDEN ZUBAIR MAITAMA | BUK, KANO
49 | YAƘIN ISRA'ILA DA IRAN DA KUMA NAHIYAR AFRICA | DR. RIYA'UDDEN ZUBAIR MAITAMA | BUK, KANO Dec 8, 2025 02:58:00 A WANNAN KASHI NA 49, MUN TATTAUNA YAKIN KWANAKI 12 TSAKANIN ISRA’ILA DA IRAN:• ASALIN RIKICIN.• TARIHIN KAFUWAR ISRA’ILA DA IRAN.• YADDA DANGANTAKA TA DIFLOMASIYYA TA RIKIDE ZUWA GABA DA ADAWA.• ME YA TAYAR DA RIKICIN YANZU.• RAWAR KASASHEN YAMMA WAJEN TALLAFAWA ISRA’ILA.• DA TASIRIN RIKICIN A NAHIYAR AFRIKA.TARE DA BABBAN BAKO: DR. RIYA’UDDEEN ZUBAIR MAITAMA — ƘWARARRE A KIMIYYAR SIYASA DA SHA’A
48 | WATA DA'AWAR SAI DA MUKABALA | IMAM ADAM IDIRS DUMI | KUNGIYAR KWARARRU MASU DA'AWA (PDM)
48 | WATA DA'AWAR SAI DA MUKABALA | IMAM ADAM IDIRS DUMI | KUNGIYAR KWARARRU MASU DA'AWA (PDM) Dec 1, 2025 02:43:36 TATTAUNAWA MAI ARMASHI KAN GWAGWARMAYAR DA’AWA GA WAƊANDA BA MUSULMI BA — MUSAMMAN KIRISTOCI DA MAGUZAWA.ZA MU BINCIKO NASARORI, ƘALUBALE, DA HAƊURRAN DA KE TATTARE DA WANNAN AIKI MAI MUHIMMANCI.BABBAN BAƘONMU A SHIRIN: SH. IMAM ADAM IDRIS DUMI, SHUGABAN ƘUNGIYAR ƘWARARRUN MASU DA’AWA, RESHEN JIHAR BAUCHI, WANDA YA SHAFE SHEKARU YANA GUDANAR DA WANNAN DA’AWAR CIKIN ƘWAREWA DA JAJIRCEWA.
47 | IZALA DAGA TUSHE (02) | SHEIKH YAKUBU MUSA HASSAN KATSINA SHUGABAN JIBWIS NA JIHAR KATSINA
47 | IZALA DAGA TUSHE (02) | SHEIKH YAKUBU MUSA HASSAN KATSINA SHUGABAN JIBWIS NA JIHAR KATSINA Nov 3, 2025 02:08:50 SHIRIN ZAI YI WAIWAYE NE A KAN TARIHIN GWAGWARMAYAR KAFUWAR KUNGIYAR IZALA, NASARORI DA KUMA KALUBALEN DA TAKE FUSKANTA, DA KUMA BADA SHAIDA A KAN DALILIN RABUWAR IZALA, TARE DA JIGO A KUNGIYAR SHEIKH YAKUBU MUSA HASSAN KATSINA.BATUTUWAN SHIRIN:

Recommended