Home Podcasts Ilimi Hasken Rayuwa
Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi Hasken Rayuwa

RFI Hausa 24 Episodes Jul 14, 2026

Wannan shirin yana fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a fannin ilimi a duniya, tare da nazari kan binciken kimiyya da fasaha da ke neman saukakawa dan'adam. Ana kuma jin ra'ayoyin masana kan yadda za a inganta rayuwar bil'adama. Shirin yana fitowa a duk ranar Talata da safe, kuma ana maimaita shi ranar Alhamis.

Episodes

Makomar ilimin yara a Kano na cikin halin rashin tabbas Jul 14, 2026 00:10:00 Shirin na wannan makon cigaba ne kan wanda muka gabatar a makon jiya, wanda ya gano yadda yara a wasu yankunan jihar Kano basa zuwa makaranta saboda yawon tallace-tallace domin tara kudin kayan ɗaki. Yayin da su kuma mazan suke diban yashi da fasa Dutse, da sunan wai su taso suna da sana'ar dogaro da kai. Yankunan da wannan lamari yafi kamari sun hada da Challawa, Kafin Maiyaki, Madobi, Gora, da K
Yadda makomar ilimin yaran karkara a Najeriya ke cikin rashin tabbas Jul 8, 2026 00:10:00 A wannan makon, shirin ya nufi yankunan karkara, inda inda gine-ginen makarantu ke ci gaba da kasancewa a matsayin kango, kasancewar babu dalibai. A wasu wuraren kuma, azuzuwan sun zama fanko, yayin da matasa da yara suka ƙaurace wa shiga, ‘yan mata na fita birni yin tallace-tallace, su kuma samari na dambatawa da aikin ƙwadagon fasa duwatsu da ɗiban yashi. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sa
Taron ƙaddamar da littafin tarihi na wani fitaccen matashi a Kanon Najeriya Jun 30, 2026 00:10:02 Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan taron ƙaddamar da sabon littafin tarihin nan mai suna 'Mu San Magabata', wanda fitaccen matashin marubuci Kabiru Ahmad Kwalli ya rubuta da aka gudanar a jihar Kanon Najeriya. Taron ya haɗa masana, sarakuna, da ɗandazon al'umma domin duba yadda za a ceto tarihin ƙasar Hausa da ke shirin bacewa. Wannan littafi, kamar yadda masana da dama suka bayyana,
Yadda aka gudanar da taron manyan masana na duniya a birnin Lagos Jun 23, 2026 00:10:00 A wannan makon, shirin ya mayar da hankali ne kan babban taron ƙungiyar Lagos Studies Association karo na goma da aka kammala a ƙarshen mako, wanda ya saba haɗa masana, malaman jami'o'i, da masu bincike daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje domin tattauna halin da ilimi yake ciki a nahiyar Afirka cikin wannan ƙarni. Wannan taro, wanda aka kafa shi shekaru goma da suka gabata a birnin
Yadda talauci ke hana ɗalibai cikar burinsu Jun 9, 2026 00:10:04 Shirin Ilimi hasken rayuwa na wanna Mako ya mayar da hankali ne kan yadda matsin tattalin arziki ke tilstawa ɗalibai haƙura da cikar burinsu na karatu, don kawai neman abin kaiwa baka, a kowacce rana. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsioyya Haruna.
Shirin kawar da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta na samun nasara a Jigawa Jun 2, 2026 00:10:00 Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya sake waiwayar matsalar nan ce ta yawaitar yaran da ba za zuwa makaranta a arewacin Najeriya, batun da a fannin ilimi ke ci wa al’ummar yankin tuwo a ƙwarya.  Masu iya magana dai na cewa ‘mai rai ba ya rasa motsi’ domin kuwa duk da girman da wannan matsala ta yi a Najeriya musamman ma yankin arewacin ƙasar, akwai waɗanda suka tashi tsaye wajen ganin sun
Ɗimbin matasa na haƙura da karatun boko saboda rashin tabbas kan samun aiki May 19, 2026 00:10:00 Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda matasa a baya-bayan na ke haƙura da ilimin boko saboda shakku kan yiwuwar samun aikin yi. Matsalar rashin aikin yi bayan shafe tsawon shekaru ana karatu tare da kashe maƙuden kuɗaɗe ya sanya matasa da dama musamman waɗanda ba ƴaƴan wasu ba ajje tunanin karatu tare da mayar da hankali a kasuwanci da koyo
An yafe wa ɗaliban da ke son shiga kwalejin ilimi rubuta JAMB a Najeriya May 12, 2026 00:09:58 A yau muna ɗauke da wani labari mai daɗi ga ɗaliban da ke sha’awar zama malamai da kuma masu son shiga Kwalejin Ilimi a faɗin Najeriya. Gwamnatin ta fitar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin sauƙaƙa wa ɗalibai hanyar neman ilimi da kuma ƙarfafa musu gwiwa ta fuskar kuɗi. Ministan Ilimi Tunji Alausa, ya sanar da cewa ɗaliban da ke son shiga Kwalejin Ilimi yanzu ba sai sun rubuta jarrabawar UTME ba.
Tasirin fasahar zamani wajen bunƙasuwar aikin jarida May 5, 2026 00:09:59 Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan bikin ranar ƴancin ƴan Jaridu ta duniya da ke gudana a kowacce ranar 3 ga watan Mayu, bikin da ke zuwa a wannan karon cikin wani yanayi da aikin na Jarida ke ganin koma baya. Akwai dai ƙorafe-ƙorafe daga sassa daban-daban kan yadda aikin  na Jarida ke fuskantar barazana kodayake masu ruwa da tsaki a wannan
Yadda makarantun tsangaya suka fara gauraya karatun addini da na Boko don tafiya da zamani Apr 28, 2026 00:09:55 Shirin Ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda makarantun tsangaya da na Islamiyya suka fara gauraya karatun addini da na zamani a ƙoƙarin da suke yi na tafiya da zamani da kuma amun tallafi daga gwamnatoci da manyan ƙungiyoyi na duniya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2 Apr 22, 2026 00:10:00 Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tamba
Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2 Apr 21, 2026 00:10:00 Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tamba

Recommended