
Ammasco Radio 90.7 FM gidan rediyo ne a birnin Kano, Najeriya, wanda Alhaji Mustapha Ado ya kafa a ranar 7 ga Fabrairu 2024 a matsayin wani bangare na ayyukan taimakon al'umma. Gidan rediyon yana watsa labarai, muhawara, da shirye-shiryen nishadi da ilmantarwa a yaren Hausa, da nufin karfafa matasa da bunkasa al'umma.